Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kashe AVM Muhammad Maisaka mai ritaya, da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a gidansa da ke Ragasi a karamar hukumar Igabi a Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a ranar Talata, a Kaduna.
Jalige, wanda ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Talata, ya kuma ga dan gidan nasa ya samu rauni sakamakon harin.
Ya ce lokacin da aka samu labarin; Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Mudassiru Abdullah ya umurci jami’in ‘yan sandan shiyya da kwamandan yankin zuwa wurin.
Karanta Haka: Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mata 4 a Suleja
“An kwashe gawar zuwa asibiti sannan kuma an garzaya da mai gate zuwa asibiti domin yi masa magani,” in ji shi, yayin da za a ba da cikakken bayani kan lamarin nan ba da jimawa ba.