Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahadi Shehu ya bayyana dalilan da suka sanya shi ya ɗauki matakin rushe gidan Rediyon Vision FM dake Kaduna da sanyin safiyar ranar Litinin.

Da yake jawabi a yayin wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna, Mahadi Shehu ya ce ya ɗauki matakin ne saboda ƙarfi da dokar kasa ta bashi a matsayin shi na mamallakin ginin gidan Rediyon, kuma ya bada shi aro ne ga Shugaban gidan Rediyon na Vision Umar Faruq Musa tun a Shekarar 2018 ba tare da ya nemi a bashi sisin kwabo ba.

“Umar Faruq Musa ya koma da baya yana cin duddugena ta hanyar amfani da ake yi da gidan Rediyon Vision na Katsina ana cin mutunci na wanda hakan ya saɓa dokar aikin jarida, kuma aka hana ni yin magana domin in kare kai na a gidan rediyon”.

Ɗan kasuwar ya kara da cewar Shugaban rediyon Vision ya cigaba da keta mishi haddi tare da nuna tamkar babu wata alaƙa dake tsakanin su, wannan ne ya sanya a matsayin shi na mai ginin da gidan Rediyon yake ya rubuta takardar neman gidan Rediyon ya tashi ya bashi wurin ta hanyar bada wa’adin shekara guda, amma a wata ziyara da ya kai gidan Rediyon sai yaga babu wasu kayayyakin da za a yi wahalar cirewa, saboda haka sai ya mayar da wa’adin zuwa watanni huɗu.

Bayan da wa’adin ya cika Umar Faruq Musa bai tashi ba, hakan ya sanya Mahadi Shehu ya zo a wata rana ya yaye rufin ginin da cire gate, inda shi kuma Umar Faruq Musa ya kai ƙara hukumar ‘yan sanda yana zargin Mahadi Shehu ya yi mishi kutse cikin gidan Rediyo.

Sai dai kuma a dukkanin zama da kwamishinan ‘yan sanda ya yi yunkurin yi a tsakanin Mahadi Shehu da Umar Faruq Musa bisa ga ƙarar da shi ya kai abin ya gagara, sakamakon kin yarda su hadu da Mahadin.

Daga ƙarshe Mahadi Shehu ya yi amfani da damar da doka ta bashi ya rusa wani sashi na ginin gidan Rediyon, kuma zai kara ɗaukar matakin da ya fi haka matuƙar Umar Faruq Musa bai tashi daga cikin ginin ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *