Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti da zai kula da ayyukan Cibiyoyin Musulunci da ke aiki a jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin din nan, inda ya ce kwamitin ne ke da Hakkin samar tsare-tsaren yadda za’a gudanar da ayyuka a Cibiyoyin.

Ya lissafa Wasu Cibiyoyin da abin zai shafa a matsayin wadanda ke bayar da tallafi a fannonin ilimi, samar da ruwan sha, gina masallatai, jin dadin gidajen marayu da sauran ayyukan addini.

Garba ya ci gaba da cewa, kwamitin ya kuma ba wa hukumar damar tabbatar da sahihancin irin wadannan Cibiyoyin na kasa da kasa, da tantance bayanansu, da takardar shaidar rajista, abokan hulda da kuma hanyoyin samun kudadensu.

Kazalika ya Kuma bayyana cewa, Babban limamin Kano Farfesa Sani Zaharaddeen da kwamishinan harkokin addini Dr Muhammad Tahar Adam ne zasu jagoranci kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilai daga kungiyoyin Qadiriyya, Izala da Tijjaniyya, ‘yan sanda, DSS, hukumar shige da fice, Civil Defence, da kuma kungiyar ‘yan banga ta Najeriya.

Sauran sun hada da kungiyar lauyoyin musulmi, ofishin kula da filaye, hukumar tsara birane da raya kasa ta jihar Kano, da ma’aikatun shari’a, ilimi, da lafiya, da kuma majalisar masarautu.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *