Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su firgita saboda karancin man fetur yayin da Kamfanin ya tanadi sama da lita biliyan 1.7 na man fetur.
A cikin sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun kamfanin na NNPC Garba Deen Muhammad, kamfanin mai na kasa ya ce, bai kamata a sanya fargabar karancin man fetur a duk lokacin bukukuwan karshen shekara ba, da ma bayan hakan ba.
“Ana shawartar jama’a da kada su shiga firgici da siyan Man, wanda aka fi sani da man fetur.”
Kamfanin mai na kasa NNPC ya bayyana hakanne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin cewa, ” NNPC na da sama da lita biliyan 1.7 na man fetur kuma ana sa ran karin kayan da za su shigo kasar a kullum cikin makonni da watanni masu zuwa.”
Sanarwar ta kuma ce, NNPC din ba ta da masaniya kan wani shiri da gwamnati za ta yi na haifar da karin farashin man fetur.
Ya ci gaba da cewa: “Saboda wannan tabbacin, kamfanin na NNPC yana shawartar masu ababen hawa da sauran masu amfani da man fetur da su ci gaba da sayan man fetur na yau da kullum ba tare da sun shiga wani yanayi na firgita ba wanda zai iya aika da wasu alamu marasa kyau a fadin kasar nan.
- “Kamafanin NNPC yana kuma jan hankalin masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da samar da Man fetur da rarraba man fetur ga kowane bangare na kasar nan a lokutan bukukuwa da kuma bayan haka.”