Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da kammala aikin titin Janguza-Durum-Kabo-Karaye da aka yi watsi da shi na miliyoyin naira, wanda aka bayar tun a shekarar 2010.

Kwangilar aikin hanyar wadda gwamnatin Sanata Ibrahim Shekarau ta fara bayar da shi kan kudi naira biliyan 3, 424, 010, 877.00, an sake duba shi zuwa Naira biliyan 7, 020, 139, 700.55, bisa la’akari da fa’idar aikin da kuma yadda al’ummar yankunan zasu amfana da shi.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da sakamakon taron majalisar mako da aka gudanar a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin Kano.

Ya ce yayin da dan kwangilar ya karbi sabon farashin kuma aka sake dawo da shi zuwa wurin kuma yana ci gaba da aiki, Ma’aikatar Ayyuka ta lura da irin karancin kudi da jihar ke fama da shi, sakamakon illar da cutar COVID-19 ta yi kan tattalin arzikin duniya da kuma sake farfado da tattalin arzikin duniya, don haka ne yasa za a sake aiwatar da aikin tare da sanya shi akan kudi N5, 605, 424, 417.44 biliyan.

 

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *