Gwamnatin APC a karkashin mulkin Shugaban kasa, Muhammad Buhari ta sanar da cewa za ta tura masu maganin gargajiya kasar sin domin su koyo sabbin hanyoyi da dibarun yin maganin cuta.
Ministan Jihohi, na bangaren fikira da fasaha, Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa;”Hukumarsa ta shirya hada hannu da gwamnatin kasar caina domin habbaka magungunar gargajiya a Najeriya. Biyo bayan hakan, za mu tura masu bayar da maganin gargajiya zuwa kasar china domin su samu ingantaccen horaswa dangane da maganin gargajiya”.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin gudanar da wani kwarya-kwaryan taron karawa juna sani da ya wakana a babban birnin tarayya Abuja wanda kungiyar Nigerian Youth Congress (NYC) ta hada domin tattaunawa da karin hasken Alakar da ke tsakanin Najeriya da China a fannin magungunar gargajiya.
Mai wakiltan kasar China a Najeriya, Ambasado Cui Jianchun ya ayyana zaguwar kasarsa na ganin ta agazawa Najeriya wajen farfado da sashin maganin gargajiya a najeriya.