Iran ta amince ta ci gaba da tattaunawa a wannan watan kan batun farfaɗo da yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa a 2015. Wannan ce tattaunawa ta farko tun bayan da aka zaɓi shugaban ƙasar mai tsatsauran ra’ayi Ebrahim Raisi a watan Yuni.
Babban jami’in Iran ɗin wanda ke wakiltar ƙasar wurin tattaunawar Ali Baqeri Kani ya bayyana cewa gwamnatinsu ta amince a soma tattaunawar a ranar 29 ga watan Nuwamba.
Bbc taruwaito Amurka ta janye daga wannan yarjejeniya ne tun a lokacin mulkin Shugaba Donald Trump, sai dai dama Amurkar ta ce akwai yiwuwar ta sake komawa domin cimma yarjejeniyar.
A halin yanzu dai gwamnatin Shugaba Joe Biden ta ce za halarci zaman wanda za a yi a Vienna tare da sauran waɗanda suka sa hannu a yarjejeniyar baya da suka haɗa da China da Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha.
Ned Price, wanda shi ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa za a yi saurin cimma wannan yarjejeniyar idan wakilan Iran da gaske suke yi.