Akwai kuma wani bangare na babban taron jam’iyyar PDP na kasa da ya kamata a yi magana a kai.
Wannan al’amari ya shafi yadda dan takarar da jiga-jigan PDP biyu ke marawa baya ya sha kaye a yayin babban taron. ‘Yan siyasar biyu da suka marawa wanda ya fadi baya, sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki. Wanda suka yi kakkausar goyon baya a cewar rahoton da Sahara Reporters ta wallafa shi ne tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola. Oyinlola ya tsaya takarar mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa (Kudu). Ya fafata da wani tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo, Taofeek Arapaja wanda Gwamnonin PDP suka mara masa baya bayan Gwamna Seyi Makide ya fifita shi a kan wannan mukami. Makinde ya shawo kan abokin aikin sa Gwamnoni su ma su marawa Arapaja baya.
Oyinlola babban jigo ne ga Atiku a tsawon shekaru. Ya kasance mai himma da taimako a lokacin zaben shugaban kasa na 2019 da Atiku ya tsaya takara. Hasali ma, don tabbatar da amincinsa, ya yi murabus daga babban mukamin da yake rike da shi a lokacin, ya shiga tawagar Atiku domin gudanar da yakin neman zabensa na shugaban kasa. Hakazalika, Saraki ya tabbatar da cewa shi ne babban abokin Atiku. A shekarar 2019 da Atiku ya fito takara a PDP, Saraki wanda ya sha kaye a zaben fidda gwani, ya yi layi a bayan Atiku. Ya zama Darakta Janar na yakin neman zaben Atiku.
A yanzu da Atiku ya goyi bayan Oyinlola mai biyayya ga mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar PDP ta Kudu ta kasa, Saraki ya goyi bayan Atiku don ganin Oyinola ya lashe zaben. An bayyana cewa har Atiku da Saraki sai da suka bar kujerunsu suka kai wa wakilan PDP neman goyon bayan Oyinlola a yayin babban taron da aka yi a Abuja. Hakan ya nuna yadda suka yi masa aiki da kuma irin kokarin da suka yi na ganin cewa dan takarar da suke so ya yi nasara. Amma, hakan bai yi nasara ba.
Hakan ya faru ne saboda Gwamnonin PDP da ke rike da tsarin jam’iyyar a jihohinsu da yankuna daban-daban sun hada kai da jiga-jigan jam’iyyar biyu. Don wannan mukami, Gwamnonin PDP sun yanke shawarar marawa wanda Makinde ke so (wato Arapaja) baya don ya ci wannan mukami. Sun yi shirye-shiryensu kuma sun tabbatar sun bi ta.
Akwai wasu dalilai guda biyu da suka sa Gwamnonin PDP goyon bayan Arapaja wanda Makinde ya gabatar. Na daya, an ce sun yanke shawarar ba za su goyi bayan tsoffin janar-janar na soja don samun manyan mukamai a jam’iyyar. An bayyana hakan a cikin rahoton The Punch. Hakan na nufin Oyinlola wanda tsohon jami’in soja ne ba zai samu tagomashi a wannan bangaren ba. Wani dalilin da ya sa Makinde da sauran Gwamnonin PDP suka goyi bayan Arapaja shi ne saboda babban masoyin Gwamnan Oyo ne.
Makinde ya gwammace ya samu mutumin nasa a wannan mukami wanda zai taimaka wajen tabbatar da rikonsa na jam’iyyar PDP a matsayinsa na shugaban jam’iyyar a yankin Kudu maso Yamma maimakon Oyinlola wanda shi ne babban masoyin Atiku ya hau kujerar. A karshe Arapaja ya lashe zaben da kuri’u 2,004 yayin da Oyinlola ya samu kuri’u 705.