Mataimakin shugaban filin wasa da sanya nishadi na Kano Club Umar Adam Kolo yace Kano Club gurine daya kunshi guraren wasanni da debe kewa, da alumma da dama basu fahimceshi ba,
A tattaunawarsa da wakilinmu salisu musa jegus, mataimakin shugaban na kano club Umar Kolo cewa yayi sabanin yadda jamaa da dama ke kallon Kano Club da cewa wajene na holewa da badala, kolo.cewa yayi ” Sam shi filin wasanni ne na manyan mutane a kasa ba jihar kano kadai ba ” inda ya kara da cewa Club wajene da manya mutane dake shugabanci a matakai daban daban kan zauna dan hutawa da motsa jiki da tattanmuna alamura cikin sirri da natsuwa,
Da yake amsa tambaya kan irin yadda rayuwa ke kasancewa a irin wannan guri Kolo cewa yayi a Club ne kadai zaka iya ganin Sarki, ko Gwamna ko Babban Jamiin soja ko Dan sanda kai har manyan sakatarorin gwamnati na jiha dana tarayya da manyan yan kasuwa da shygabannin kamfanoni ba tare da shamaki ba matukar kana cikin club din kuma zasu saurareka saboda darajar club din harsu taimakeka idan bukatar hakan ta taso,
Adam Kolo wanda ya lasafta wasannin da filin ke dauke dasu kamar Tennis , Scrabble, Chess, Table Tennis, Golf da sauransu yace lokaci yayi da alumma zasu fahimci mahimmanci club da irin tasirin da yake dashi na hada zumunta da taimakon juna,
Kolo.ya kara da cewa tun a shekarar 1970 kano club ke samun jagoranci da cigaba da bunkasa rayuwar mutane a fanonin daban daban,
Ya kara da cewa matasa da dama sun sami ayyukan yi a hukumomin tsaro na soja da Dan sanda har dana farin kaya ta hanyar kano club wanda haka ke zama abin alfahari da jin dadi ga kowa da kowa musamman shugabanci cibiyar,
Dan gane da gasar Dala Hard Court Tennis da ake gudanarwa shekaru 33 dasuka gabata kolo cewa yayi gasar abar alfaharice ga kowa musamman ma dayake a kano club kadai ake yinta, ” Ta daga darajar kano club kuma zamu cigaba da bata goyon baya muna alfahari da ita ” inji Umar Kolo