Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A yayin gwamnatoci da hukumomi ke kokarin tabbatar da inganta tsaro dan kyautatuwar jin dadi da bunkasa tattalin arziki tsakanin alumma,

Shugaban karamar hukumar Tarauni Abubakar Zakari Habu P.A ya bukaci jamian tsaron sa kai, Dagatai da Masu Unguwanni na yakin dasu rubanya kokarinsu na samar da tsaro a fadin karamar hukumar,

Habu P.A ya bayyana hakane yayin taron wayar da kan alumma da kaddamar da kwamitin tsaro da bada Baburan Sintiri da kyautata tsaro da jin dadin Alummar yankin da aka gudanar a dakin taro na hukumar hisba na karamar hukumar, tare da hukumomin tsaro na yan sanda, Immigration, Civil defence, Dss da kungiyar Vigilante dake fadin karamar hukumar,

Habu P.A wanda ya yaba da yadda alumma suka amsa kira dan halartar taro, ya ja hankalin masu bada Haya da sayar da gidaje ga bakin haure da wadanda baa sani ba, dasu daina har sai sun tantance su tare da sanar da mahukunta,

A jawabinsa hakimin Tarauni Sarkin Fadar Kano Malam Ado Kurawa kira yayi ga alummar Tarauni dasu hadan karfi da karfe tare da yan kungiyar tsaron sa kai na karamar hukumar da dagatai da masu unguwanni da cimma burin da akasa a gaba

Da yake jawabi daraktan mulki na karamar hukumar wanda babban jsmii mulki na karamar hukumar ya wakilta …..godewa shugaban karamar hukumar yayi bisa hangen nesansa kan harkokin tsaro da kyautata cigaban alummar yankin

Da yake jawabi a madadin yan kwamitin shugaban kwamitin tsaron Alhaji Garba Danjuma ya shaalwashin yin aiki tsakani da Allah tare da bada dukkan hadin kai ga shugaban karamar hukumar da cimma nasarar da akasa a gaba,

Daga cikin wadanda suka harci bitar sun hadar da tsofin shugabannin karamar hukumar da masu ruwa da tsaki, shugabannin siyasa, zababbun kansiloli da masu gafaka, Dagatai masu unguwanni, yan Vigilante da sauran alumma

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *