Shugaban kwamitin bunkasa wasan kwallon kafa na hukumar wasan kwallon kafar najeriya Comrade Ahmed Yusif Fresh yace daga lokacin da ya jagoranci kwamitin bunkasa wasan kwallon kafa a najeriya zuwa,yanzu akwai gagaruni sauyi da cigaba da kowa ke gani a fili,
A wata tattaunawa ta musamnan da wakilin gidan radiyon express dake jihar kano a arewacin najeriya salisu musa jegus, shugaban kwamitin Ahmed Yusif Fresh ya bayyana irin nasarori da bangaren bukasa wasan kwallon kafa na kasa ya samu, musamman yadda ake zakulo yan wasa matasa masu kananan shekaru kamar 13 da 15 zuwa 17 da yan 20 daga ko Ina a fa din kasarnan inda ake horar dasu daga mataki zuwa mataki abin daya bawa da dama daga cikinsu damar kaiwa wani matsayi da kowa ke alfahari dashi a yanzu,
Fresh wanda ya bada misalin da yadda suka kyautata tsarin samar da yan wasa matasa a shekara ta 2013 inda kungiyar yan kasa da shekaru 17 ta kasa ta taka rawar gani da kowa yake alfahari da ita a najerya da afrika, ya bada misali na yadda kungiyar ta samar da yan wasa cikinsu harda Kelechi Ehinacho wanda a yanzu ke dafe miliyoyin kudade a duk mako irin kudaden da babu wani maaikaci na gwamnati dake samunsu,
Shugaban kwamitin Fresh ya Kara da cewa aiki da kwamitin yakeyi wani abune da yake haska irin kyawawan manufofin hukumar wasan kwallon kafa ta kasa da irin burin da hukumar ke dashi na ganin an inganta harkokin wasan bisa doron dokar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA,
Fresh wanda shine shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta jihar Niger dake yankin arewa ta tsakiya yace hukumar wasa ta kasa na alfahari da yadda cigaban wasan ke kasancewa laakari da yadda najeriya ke samar da matasan yan wasa zuwa kasashen daban daban a nahiyar turai,
Da yake amsa tambaya kan rahotannin dake cewa rasuwar Coach Danladi Nasidi ( ALALA ) ta kawo koma baya wajen zakulo.kananan yan wasa a najeriya Fresh cewa yayi ” E gaskiyane an samu koma baya saboda kwarewarsa da sadaukar kai da yake da su, amma ai akwai mataimakinsa Ilerika, ga Haruna Ilerika dama tare suke aiki kuma maimakon mu baiwa wani sai muka bashi kuma yana kokari kwarai”
Dangane da sauyin fasalin bunkasa wasan kwallon kafa a najeriya Sardaunan kwallon kafa cewa yayi ” salisu ! kwallon kafa dokoki ne da ita kuma bisa wadannan dokokin muke kamar yadda hukumar wasan kwallon kafa ta duniya ta tsara ”
Kan yadda a kullum yake ziyartar jihar kano Ahmed fresh cewa yayi ” Inason kano saboda mahaifar iyayena ce, Asalina Kura cibiyoyinmu na kura, iyayen mu zaman kasuwanci ne ya kaisu Niger suka haifemu dan haka nima dan kano ne”
Dayake bayyana yadda wasan kwallon kafa yake jihar kano fresh cewa yayi hukumar wasan kwallon kafa ta jihar kano ta ciri tuta wajen yadda take tsare tsaren ta, da yadda take jan manyan mutane cikin harkokin ta abin sai godiya, “kuma inaso kullum jihar kano ta zama ta daya a wasan kwallon kafa saboda yadda jamaar jihar keson wasan fiye da ko ina”
Inji fresh,
Inda ya Kara da cewa cigaban wasan a najeriya ya karu laakari da yadda ake samun yan wasa da kasashen turai ke son dauka da sauran kasashe a fadin duniya,wanda haka abin alfaharine garemu.