Gwamnatin jihar Kaduna ta soke amfani da babura, sannan kuma ta takaita wuraren da babura masu kafa uku za su rika shiga, domin kawo karshen rashin tsaro da ke neman wuce gona da iri in ji sanarwar,
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya sanar da haka, inda yace matakan haramcin da zai dauki tsawon watanni uku zai fara aiki daga ranar Alhamis 30: ga watan Satunba na wannan shekarar 2021: da muke ciki inda aka takaita babura masu taya uku aiki daga karfe 6: na safe zuwa 7: na yamma,
Aruwan yace tuni gwamnatin tarayya ta toshe layukan sadarwa a wasu yankuna jihar, bisa bukatan hukumomin jihar Kaduna har sai baba ta gani, in ji shi,
A cikin matakan da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka sun hada harda mallakar makamai ga al’umma,