Daga Abbakar Aleeyu Anache,
Bangaren marasa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya ya caccaki jawabin da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar a zauren majalisar Dunkin Duniya yayin taron da aka kammala a ranar Asabar, inda suka ce mayakan Boko Haram sun kara karfi a zamanin shugabancin sa, sabanin ikirarin da yayi na kassara su,
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban marasa rinjayen majalisar wakilan Najeriya Ndudi Elumelu, ya ce jawabin da Buhari yayi a taron majalisar Dunkin Duniya karo na 76: yayi hannun riga da gaskiyar halin kuncin da gwamnatinsa, ta jefa yan Najeriya a ciki, na fuskantar koma bayan tattalin arziki, tsaro da zamantakewa,
A cewar Elumelu, sun kadu da ikirarin da Shugaban Najeriya kan cewa yan ta’adda sun yi rauni matuka a karkashin mulkinsa, ta yadda a yanzu ba sa iya kaddamar da munanan hare-hare, bayan kuma cewa a zahiri ba haka abin yake ba,
Bangaren marasa rinjayen majalisar wakilan Najeriya ya kuma koka kan yadda jawabin Shugaba Buhari, bai bayyana satar daliban da yan bindiga ke yi daga makarantu a sassan arewa maso yammacin kasar ba, lamarin da ya gurgunta sha’anin ilimi saboda tilasta rufe makarantu da dama,
Yan majalisar sun yi ikirarin cewa a halin da ake ciki, masu tayar da kayar baya na kai farmaki kan sansanonin sojoji, kashe mutane da yin garkuwa da wasunsu gami da mamaye garuruwa ba tare da an murkushe su ba