Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekara 25, bisa zarginsa da aikata Fasikanci da Akuya a karamar hukumar Gwaram.

Kakakin Rundunar ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, a Dutse cikin wata sanarwa.

A cewar ASP Shiisu Adam ya ce Ofishin hukumar ne na karamar hukumar Gwaram ya kama mutumin da misalin karfe 1 na Dare a lokacin da suke sumame.

Rundunar ta ce ta kama mutumin wanda Mazaunin Unguwar Kunnadi ne lokacin da yake tsaka da aikata lalata da Akuyar.

Kazalika, ya ce rundunar tana cigaba da zurfafa bincike kan Lamarin kafin ta gurfanar da shi a gaban Kotu.

Sashe na 214 na Kundin Manyan Laifuka ya yi hani da aikata Lalata da Dabbobi, inda Dokar ta tanaji hukuncin shekaru 7 a Gidan Yari.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *