Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar yan sandan jihar jigawa tayi nasarar kama wani mutum ɗan shekara 25, bisa zarginsa da aikata fasikanci da akuya a karamar hukumar gwaram.

Kakakin Rundunar ASP Lawan shiitu Adam, shine ya bayyana hakan ga kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, a Dutse cikin wata sanarwa.

A cewar ASP Lawan yace ofishin hukumar ne na karamar hukumar Gwaram ya kama mutumin da misalin karfe 1 na dare a lokacin da suke sumame.

Rundunar tace ta kama mutumin wanda mazaunin Unguwar kunnadi ne lokacin da yake tsaka da aikata lalata da Akuyar.

Kazalika, yace rundunar tana cigaba da zurfafa bincike kan lamaran kafin ta gudanar da shi a gaban kotu

Sashe na 214 na kudin manyan laifuka yayi hana da aikata lalata da Dabbobi, inda Dokar ta tanaji hukuncin shekaru 7 a Gidan Gyaran Hali.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *