Faransa ta gargadi Mali akan shirin dauko sojojin hayan kamfanin Wagner daga Rasha mutum dubu guda domin taimakawa kasar yaki da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi da suka addabe ta.
Gargadin ta bakin ministar tsaron Faransar Florence Parly bayan fitar bayanan da ke cewa bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar daukar Sojojin hayar na kamfanin Wagner mai zaman kansa a Rashan don yaki da matsalar tsaron da Mali ke fuskanta, ta ce matakin zai iya shafar alakar su da kasar.
Ministan tsaron ta Faransa ta ce kulla makamanciyar yarjejeniyar zai zama babban koma baya ga kasar ta Mali wadda ke ci gaba da samun tagomashin taimakon yaki da ayyukan ta’addanci daga uwar goyonta Faransa tun bayan tsanantar ayyukan ta’addanci a kasar cikin shekarar 2012.
Faransa dai na da dakaru na musamman a kasashen Sahel wadanda kusan dukkaninsu ke fama da matsalar tsaro, sai dai akwai zarge-zarge da al’ummar kasashen ke yi, da ke alakanta uwar goyon ta su da rura rikici a kasashen koma daukar nauyin ayyukan ta’addancin dungurugum.
Tun bayan juyin mulkin Soji a kasar ta Mali alaka tsakanin kasar ta Faransa uwar goyonta ya fara raunata, bayan banbantar ra’ayoyi a yaki da ayyukan ta’addanci.
Kakakin ma’aikatar tsaron Mali da ya ke amsa tambaya kan zargin, ya ce har zuwa yanzu ba su kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyar da kamfanin na Wagner ba, sai dai suna ci gaba da tattaunawa kan matakan da za su dauka don tunkarar matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar.
Kamfanin na Wagner mai zaman kansa da ke Rasha ya yi kaurin suna wajen bayar da Sojojin haya don tallafawa a yakin da ya ki ci yaki cinyewa inda aka ga rawar da suka taka a rikicin kasar Syria da kuma Libya.
Shigar Sojin hayar na Wagner Mali zai zama babbar barazana ga Faransa wadda dakarunta ke yankin Sahel tun shekarar 2013.