Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa an kashe jagoran reshen Afirka ta Yamma na kungiyar ISIS, wato ISWAP, Abu Musab Al-Barnawi.

Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa an kashe shi ne a karshen watan Agustan bana. Al-Barnawi dai dan Muhammad Yusuf ne, mutumin da ya kirkiri kungiyar Boko Haram.

A 2009 jami’an tsaro suka kashe mahaifinsa lokacin da kungiyar ta fara yakar hukumomin Nijeriya.

Akwai ruwayoyi biyu a kan yadda aka kashe Al-Barnawi.

Wata ruwayar ta ce sojojin Najeriya ne suka kashe shi, yayin da dayar kuma ta ce ya mutu ne yayin wani fadan cikin gida a tsakanin wasu bangarori na kungiyar ta ISWAP da ba sa ga maciji da juna.

Ruwaya ta farko dai ta ta’allaka ne a kan wani bayani da wasu jami’an tsaro a bakin daga suke yadawa a tsakaninsu, wanda ke nuna cewa wani kwanton-bauna sojoji suka yi da ya kai ga kashe shi da wasu manyan kwamandojin ISWAP biyar da ma mayaka da dama wadanda suka yi masa mubaya’a.

Wata majiya ta ce an kashe shi ne a Bula Yobe, wani gari da ke kusa da iyakar jihohin Borno da Yobe a tsakanin Mobbar da Abadam.

Amma wasu majiyoyin sun shaida wa Daily Trust cewa rikicin shugabanci ne ya yi ajalin Al-Barnawi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *