Akalla fursunoni 240 ne suka tsere daga gidan yarin Kabba da ke jihar kogi a tarayyar Najeriya biyo bayan wani farmaki da tsakaddare da ba a kai ga gano wadanda ke da alhakin kaddamar da shi ba.
Tuni dai hukumar kula da gidajen yarin Najeriyar ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Mr Francis Enobore inda cikin wata sanarwa ya bayyana cewa wani gungun ‘yan bindige rike da makamai ne suka afkawa gidan yarin da tsakaddare.
Kwanturolan hukumar Halilu Nababa ya bukaci daukar matakin dawo da wadanda suka tsere daga gidan yarin baya ga tsananta bincike don gano masu hannu a harin cikin gaggawa.
Haka zalika hukumar ta bukaci al’ummar jihar da makwabtanta su bayar da hadin kai wajen kai bayanan duk wasu da suke zargi ga mahukunta don mayar da fursunonin gidajen yarin.
A shekarar 2008 ne Gwamnati ta samar da gidan yarin na Kabba da ke daukar mutane 200 yayinda yanzu haka ya ke dauke da mutane 294 ciki har da 224 da ke jiran shari’a yayinda 70 ke matsayin ‘yan gidan yarin na hakika.