Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Jahar Kaduna ta umarci dukkanin Shuwagabannin Makarantun Gwamnati dana Yan Kasuwa ciki harda Islamiyyu, dasu kafa Kwamitin tsaro a Makarantun su domin kula da Lafiyar Dalibai.

Umarnin na zuwane a dai-dai lokacin da Gwamnatin Jahar ta amince da taswirar karatu ta zangon Farko na Karatun Shekarar 2021/2022, domin baiwa Makarantu damar sake budewa a kashi-kashi, a ranar 12 ga watan Satumba ta Shekarar 2021.

Kwamishinan Ilmi na Jahar Shehu Usman Muhamma a cikin wani jawabi daya fitar a ranar Asabar, ya umarci mambobin Kwamitin tsaro na Makarantu dasu tabbatar suna duba tsaro a Makarantun su gami da gaggawar sanar da wani motsi na Matsalar tsaro.

Yace idan har akwai wani kokwanto akan tsaro, to zasu iya Kiran lambar Wayoyin da aka basu.

Ya kara dacewa, Ma’aikatar na godiya da irin goyon baya da hadin kai na masu ruwa da tsaki a bangaren ilmi, da Hukumomin tsaro, da iyaye gami da Kafafen Yada Labaru, tare da yin kira a garesu, da kada su gajiya wajen ganin an tabbatar da tsaro ga masu koyo a dukkanin matakai a Jahar.

“Ma’aikatar ilmi tana umartar dukkanin Shuwagabannin Makarantu dasu yi wani tsari, na karbar Yan JSS1 da JSS2 da SSS1 da Kuma SS2 na Makarantun Sakandire ta Kwana a ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba na Shekarar 2021, da kuma na Jeka ka dawo a ranar 13 ga watan Satumba na Shekarar nan, domin karatu na tsawon Makonni 14.

Yan Firamare 1 zuwa 6 zasu dawo Makarantu, a ranar 27 ga watan Satumba na Shekarar 2021 domin karatu na tsawon Makonni 12,”inji shi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *