Gwamnan jihar Sakkwato Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewar, da yardar Allah jam’iyyar su ta PDP ce zata yi galaba a zaben 2023 dake karatowa.
Gwamnan Tambuwal wanda shi ne shugaban dandalin gwamnonin Jam’iyyar PDP na Najeriya ya bayyana hakan ne a ranar laraba a lokacin da suke taron tattaunawa da duka gwamnonin jam’iyyar 13 a gidan gwamnatin jihar Akwa-Ibom dake birnin Abuja.
Alhaji Aminu Waziri ya bayyana irin yadda jam’iyyar su ta PDP ta sami karbuwa hannun yan Najeriya wanda suke alfahari da zaben ta.
Gwamnonin na PDP sun tattauna ne akan kokarin shawo kan rikicin da ya addabi jam’iyyar da kuma tattaunawa kan batun kwamitin gudanarwar zartarwar jam’iyyar wanda za’a yi a ranar alhamis 9 ga watan Satumba 2021.
Gwamna Aminu Tambuwal ya bukaci dukkan mambobin jam’iyyar su kara himmatuwa wajen dawo da martabar su da kuma kokarin sanin dubarun murkushe APC a zaben gaba na 2023.