Gwamnan yayi wannan jawabin ne yayin gudanar zaman tattaunawa majalissar harkokin sufuri na jihar dan bayyana sabunta aikace aikacen hukumar dan tai makawa kalubaken sufuri da ake fama dashi da kuma kasuwanci.
Jawabin wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna gawmnan yace Jihar kano tana so ta bunkasa harkar sufuri dan aiwatar da cigaba wajen jan hankalin ‘yan kasuwa suzo su zuba jari.
“Sannan hakan zai gagarumin taimako wajen rage cunkoson ababen hawa tare da bun kasa cigaban kasuwanci musamman ma a cikin kwayar birni”, a cewar sa.
Anasa bangaren ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa dama wannan kudurin na harkar sufuri na kasa tuni ‘yan majalissu sun kafa kwamitin wanda mataimakin shugaban kasa yake jagoran ta wanda majalissar zartarwa ta kaddamar..