Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo a ranar Alhamis, ya dorawa Manyan Nigeria alhakin kawo tabarbarewar Matsalar Tsaro a Nigeria.

Acewar sa, ana ruruta wutar Matsalar a Kasar, ta hanyar nuna Kabilanci da bangaranci, da Maganganu marasa kamun Kai.

Osinbajo yayi jawabi a wani taro na bada lambar girmamawa a Abuja Mai taken “Matsalar Tsaro a shiyya da Kasa: gudunmuwar Yan siyasa da Wanda ba Yan siyasa ba wajen bunkasa zaman lafiya.

Yace fadin munanan kalamai akan aikace-aikacen Gwamnati da Manyan Kasar suke yi, ba tare da lura ba, shine ya haifar da ta’addanci.

Yace za’a iya magance Matsalar tsaro a dukkanin sassan kasar, idan Manyan Kasar da sauran Yan Nigeria suka dawo da sasanci a tsakanin su.

Mataimakin Shugaban Kasar ya jaddada cewa, Manyan Kasa basu da kama kai, idan yazo ga maganar magance Matsalar tsaro.

“Wasu Manyan bazasu iya zuwa ayi sasanci idan abun ya shafi Matsalar Tsaro,” inji shi, yana mai Kara dacewa, da yawa daga cikin Manyan Kasa na inganta kudirorin su na Kabilanci da bangaranci.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *