Akalla an sace fasinjoji goma sha takwas da ke kan hanyarsu ta zuwa Legas daga jihar Ondo.
Fasinjojin, wadanda ke tafiya a cikin wata mota kirar Toyota Hiace, an ce an sace su ne a Idoani-Ifira Akoko a karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Gabashin jihar.
Kazalika rahoton da Jaridar Dimokuraɗiyya ta samu ya ce, maharan sun kutsa cikin daji da waɗanda suka sacen bayan sun sungume su inda suka bar motar a kan titi.
Jami’in ƴan sanda na Isua Akoko, Hakeem Sadiq ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
Sadiq ya ce an kai rahoton lamarin ga ƴan sanda kuma tuni sashen yaki da satar mutane yana aiki tare da sauran hukumomi da yan uwan waɗanda aka sacen don ganin an ceto matafiyan ba tare da sun ji rauni ba.
Dimokuraɗiyya!