Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci hafsoshin tsaron kasar da su gaggauta kawo karshen ’ Yan bindigar da suka addabi jama’ar kasar da kuma duk wasu matsalolin tsaron da ake fuskanta.
Yayin ganawa da shugabannin hukumomin tsaron dangane da gagarumin aikin da sojoji suka kaddamar a Jihar Zamfara da zummar murkushe ‘Yan ta’addan da suka hana jama’a zaman lafiya, shugaban wanda ya yaba da rahotannin da yake samu, ya bukaci hafsoshin da su kara kaimi wajen gaggauta murkushe ‘Yan bindigar.
Ministan tsaro Janar Bashir Magashi yace sun yiwa shugaban bayani akan yadda yakin ke tafiya a Jihar Zamfara da kuma irin nasarar da suke samu domin kawo karshen illar da ‘Yan bindigar suke yiwa fararen hula.
Ministan yace shugaban kasa Buhari ya kara musu kaimi wajen ganin sun samu nasarar aikin da suke yi, yayin da ya bukaci ci gaba da azama wajen ganin aikin ya kammala cikin kankanin lokaci domin baiwa jama’a damar ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum kamar yadda aka saba.
Janar Magashi yace a nasu bangare za suyi iya bakin kokarin su wajen ganin sun kammala aikin cikin lokaci lura da kayan aikin da suke da shi da kuma goyan bayan da suke samu.
A karshen makon da ya gabata ne sojojin Najeriya suka kaddamar da munanan hare hare a sansanonin Yan bindigar dake Jihar Zamfara, bayan katse layukan sadarwar Jihar, kuma rahotannin dake fitowa na nuna cewar dakarun na samun nasara akai.