Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Yan ta’adda da suke addabar Mazauna Zamfara tare da sanyawa dole a kulle Makarantu, sun maida wasu azuzuwa domin amfanin kansu a yankin Arewa Maso Yamma.

Majiyar Jaridar Dimokradiyya ta Daily trust ta gano cewa, Makarantun Firamare da dama a kauyuka, Yan ta’adda sun Karbe ikon Makarantun.

Dalibai da Malamai sun kyale Makarantun a dalilin aikace-aikacen Yan ta’adda.

Acewar Mazauna yankin, wani Shugaban Makarantar Firamare ta Karamar Hukumar Birnin Magaji na daya daga cikin wadanda Yan ta’adda suka taba zuwa, suka bukace shi daya kulle karatu domin suna son suyi bacci a Azuzuwan.

Ba tare da bata lokaci ba da sanin abinda ka’iya biyowa baya sabudda kin bin dokar, yayi sauri ya kulle Makarantar tare da umartar Dalibai su tafi gida.

Jaridar Daily Trust ta lura dacewa, an kashe Yan ta’adda da dama a yayinda suke hutawa a Azuzuwan da makarantun ke kulle a Fadin Jahar.

Baya ga haka, akwai Makarantun da Lamarin rashin Malamai ya shafa, domin da yawansu sunki amincewa a turasu Makarantun kauyuka, sakamakon Matsalar dake tattare da zuwa koyarwar.

Wannan ne ya sanya aka bar Makarantun ko kuma rashin Malamai ya haddasa wannan Matsalar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *