Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rahotanni sun ce wani jami’in gwamnatin Najeriya, Christopher Orji, ya kashe kansa a Abuja.

Orji, mai shekaru 59, ya kasance mataimakin darakta a Hukumar Ci gaban Kimiyya da Fasaha ta Kasa (NABDA).

Ya kasance mai kula da Cibiyar Bioresource na hukumar a Langtang, Jihar Filato.

An gano gawar Orji tana rataye da igiya da aka daure da fankar rufi a gidansa da ke Ginin Gidajen Gwamnatin Tarayya, Lugbe.

Rundunar ‘yan sanda na binciken yanayin da ke tattare da rasuwarsa, in ji Dailytrust.

Orji ya mutu a ranar da ake sa ran zai amsa gayyatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC).

Mukaddashin shugaban sadarwa da ladabi na NABDA, Nkiru Amakeze ya ki yin sharhi akan lamarin.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *