Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A yammacin ranar talata ne kungiyar Najeriya ta Super Eagles ta lallasa kungiyar Cape Verde Islands daci 1-2 a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya na Qatar 2022. Fagenwasanni.com ta rahoto.

Bayan mintuna 19 da fara wasan dan wasan Cape Verde ya sanya tawagarsa a gaba, inda dan wasan gaban Najeriya Osimhen ya farke wannan kwallo a minti na 29, haka zalika a mintuna 76 dan wasan Cape Verde yaci gida inda jumulla aka tashi Najeriya na da ci 2, Cape Verde na da ci 1.

Wannan wasan ya sa kaftin din Super Eagles wato Ahmed Musa ya wakilci kungiyar har wasanni 100, kuma hakan yasa ya karbi babbar kyautar daga shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya.

Shugaban NFF waton 𝘼𝙢𝙖𝙟𝙪 𝙥𝙞𝙣𝙣𝙞𝙘𝙠 ya baiwa Ahmed Musa kyautar Naira miliyan 10 bayan ya bugawa Najeriya (Super Eagles) wasanni 100.

𝘼𝙢𝙖𝙟𝙪 𝙥𝙞𝙣𝙣𝙞𝙘𝙠 yakara da cewa” Za mu ci gaba da bayarda wannan karamci tare da girmama ‘yan wasanmu da suka buga wasanni 100 daga yanzu. Inji- Amaju Pinnick ”

Ahmed ya fara wakiltar Najeriya tun yana dan shekaru 17, a shekarar 2010, ya zura kwallaye 15 a cikin wasanni 100 da ya buga.

Yanzu yana da shekaru 28 a duniya, bayan ya taimakawa Super Eagles ta lashe gasar cin kofin Afurka na shekarar 2013.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *