Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta ziyarci Cape Verde domin buga wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya.
Bbc taruwaito cewa wannan shine wasa na bibiyu na cikin rukuni na uku da za su fafata domin neman gurbin shiga gasar da za a yi a Qatar a 2022.
Ranar Laraba 1 ga watan Satumba Cape Verde ta tashi 1-1 a gida da Afirka ta tsakiya a wasan farko na rukuni na uku.
Ita kuwa Super Eagles ta doke Laberiya 2-0 ranar Juma’a 3 ga watan Satumba a Legas, Najeriya.
Najeriya da Cape Verde sun kara a wasan sada zumunta ranar 9 ga watan Janairun 2013, inda suka tashi 0-0.
To sai dai Super Eagles ta je Cape Verde ba tare da ‘yan wasanta da ke taka leda a Birtaniya da suka doke Liberiya ranar Juma’a.
‘Yan kwallon sun hada da Wilfred Ndidi da Kelechi Iheanacho da Alex Iwobi da Oghenekaro Etebo da William Troost-Ekong da Joe Aribo da kuma Leon Balogun.
‘Yan wasan ba su sami damar zuwa Cape Verde ba, bayan da kasar take cikin wadanda Birtaniya ta ayyana daga cikin masu hadarin kamuwa da cutar korona.
Kuma duk wanda ya ziyarci kasar da Birtaniya ta ayyana mai hadarin kamuwa da cutar korona zai killace kan sa da zarar ya koma Ingila.
Hakan zai sa wasu ‘yan kwallon ba za su buga wa kungiyoyin su wasa biyu a Premier League ba da daya a Champions League