Gwamnatin jihar Katsina ƙarkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, ta kafa dokar hana sana’ar cajin wayoyi a wasu ƙananan hukumomi goma sha tara (19).
Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a gidan gwamnatin jihar yayin ƙaddamar da kwamitin da zai sa ido a kan dokar nan ta lalubo zaman lafiya da ya sa ma hannu a satin da ya gabata.
Kamar yadda Gwamnan ya lissafo, ƙananan hukumomin da wannan sabuwar dokar ta shafa sun haɗa da:
Kaita, Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Faskari da Sabuwa.
Sauran ƙananan hukumomin sun haɗa da:
Funtua, Dandume, Bakori, Danja, Malumfashi, Kafur, Musawa da Matazu.
Haka zalika dokar, kamar yadda Gwamnan ya bayyana zata haɗa da ƙananan hukumomin Dutsin-ma, Kurfi da kuma Mai’adua.
Kamar yadda Katsina Post ta rawaito, a cikin jawabin na Gwamnan, ya kuma bayyana cewa, a Karon farko, gwamnatocin jihohin dake makwabtaka da dajin rugu, sun daki alkibla ɗaya wajen tunkarar ta’addancin da ya addabi jihohin na Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna da Naija.
Gwamnan ya ƙara da cewa, “a yanzu, babu wani abu da gwamnati ta tasa a gaba irin dawo da zaman lafiya tabbatacce a fadin wannan jiha”.
Ya kuma yi kira ga ‘yan wannan kwamiti da suyi amfani da matakin ba-sani-ba-sabo wajen gudanar da wannan aiki, Sannan kuma suyi ƙoƙarin wayar da kan al’umma kan muhimmancin da ke akwai wajen haɓɓaka wadannan dokoki, domin an kafa su ne domin ceto rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su daure su ci gaba da tona asirin masu kai ma ‘yan ta’adda bayanai (informers) da kuma masu kai masu kayan amfanin yau da kullum.
Ta bangaren Shugaban kwamitin Alhaji Sanusi Buba, wanda kuma shi ne Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Katsina, ya tabbatar wa Gwamna Masari cewa za suyi duk abinda ya kamata domin ganin an cimma burin kafa wannan dokoki, wanda shi ne dawo da zaman lafiya a cikin jihar ta Katsina.