Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Idan kungiyar Nigeria (Super Eagles) ta buga wasan ta da Cape Verde Ahmed Musa zai bugawa Najeriya wasanni 100. Fagenwasanni.com ta rahoto.

Kaftin din na Super Eagles mai shekaru 28 ya zura kwallaye 15 cikin wasanni 99 daya bugawa Najeriya na baya.

Kawo yanzu yan wasan da suka wuce gabansa a jagorantar kungiyar sune:

Tsohon mai tsaron ragar Super Eagles, Vincent Enyeama ya buga wasanni (101),
Tsohon mai tsaron bayan Super Egales Joseph Yobo ya buga wasanni (101).

Ya fara bugawa Najeriya wasan farko tun yana dan shekara 17 a 2010.

Ya halarci gasannin kofunan duniya 2 na Najeriya (2014 da 2018)

Sannan ya kasance Memba, daya daga cikin yan wasa Super Eagles na ƙungiyar Afcon da sukai nasara lashe gasar a 2013.

Yana da mafi yawan ƙwallaye a raga ga Super Eagles (4) a Kofin Duniya.

Dan Najeriya na farko da ya ci kwallaye 2 cikin kofunan duniya biyu a jere.

Shin Ahmed Musa yana da damar sake kafa wadansu tarihi anan gaba?

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *