Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya jagoranci rantsar da Sakararen gwamnati, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, kwamishinoni ashirin da daya da sauran masu mukamai.

Nan take bayan shan rantsuwar, gwamnan ya bayyana ma’aikatun da kowane kwamishina zai jagoranta kamar haka :

1. Abubakar Ibrahim – ayyuka da sufuri

2. Garba Dahiru – masana’antu

3. Abdulhamid Nuruddeen – Ma’adinai da albarkatun Kasa

4. Jidauna Tula Mbami -Noma

5. Dayyabu Chiroma- sadarwa da yada labarai

6.Ahmed Aliyu Jalam – albarkatun ruwa

7. Maryam Garba Bagel – Makamashi, kimiyya da fasaha

8. Umar Babayo Kesa- Addinai da walwala

9. Adamu Manu Soro – Matasa da wasanni

10. Asma’u Giade – Al’adu da yawon bude ido

11. Hajara Gidado – Harkokin mata da yara

12. Usman Abdulkadir Modibbo – Kudi

13. Samaila Dahuwa- lafiya

14. Saadatu Bello Kirfi – kananan sana’oi

15. Aminu Hammayo- kasafi da tsare tsare

16.Yakubu Barau Ningi – Filaye da safiyo

17. Hamisu Muazu Shira – gidaje da muhalli

18. Abdulkadir Abdulhamid – Sharia

19. Usman Tilde – ilimi

20. Abdurrazak Nuhu Zaki – kananan hukumomi

21. Abdullahi Musa -ayyuka na musamman da inganta birane

Da yake jawabi yayin bikin rantsuwar, gwamnan ya taya sabbin masu mukaman murna tare da kira gare su da su yi aiki tukuru bisa doka da oda don ciyar da jihar Bauchi gaba.

Gwamnan sai yayi amfani da damar wajen kira ga kwamishinoni da su yi aiki tare da ma’aikatan ma’aikatun su inda ya bada tabbacin taimaka musu sauke nauyin dake kan su.

Gwamnan Bala sai ya jaddada aniyar gwamnatinsa na cigaba da bunkasa jihar Bauchi ta hanyar samar da ayyuka dake sauya rayuwar al’uma.

Yace adawa maras tushe da kushe ba zai karkatar da hankulan jami’an gwamnatin sa ba wajen gina jiha.

Da yake jawabi a madadin masu mukaman, Sakataren Gwamnatin jiha Alhaji Ibrahim Muhammad Kashim yabawa gwamnan yayi tare da gode masa kan zabo su don aiki wa jihar su.

Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yada labarai na zamani
2 Satumba, 2021.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *