Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daya daga cikin wadanda akayi ittifakin na taimakawa wajen bunkasa cigaban kungiyoyi da yan wasan kwallon kafa a jihar kano Salisu Musa Jegus ya comma yarjejeniyar aiki da  sanya hannun  a matsayin Daraktan wasanni a kungiyar Gaida United a jihar kano najeriya,

Gaida United na daya daga cikin kungiyoyi da zasu fafata a gasar Tofa Firimiya babbar gasa da jihar kano bayan samun nasarar shiga gasar datayi daga rukuni na daya,

A jawabinsa ga manema labarai yayin kaddamar da sabon daraktan wasan a filin kungiyar shugaban Gaida United Alhaji Kabiri Haruna Mahuta  wato KB  Mikel cewa yayi mun yanke shawarar dauka Salisu Jegus a matsayin daraktan wasa saboda yadda tarihinsa na bunkasawa da samarwa kungiyoyin da yayi aiki dasu a baya da irin cigaba da dauka daya kawowa kungiyoyin da yayi aiki dasu a shekarun baya

Kabiru ya kara da cewa Salisu Jegus mutum ne da tarihi ya tabbatar bashi da son zuciya ko nuna banbanci a lokacin da yake gudanar da aikinsa, ga kawaici da kana’a kuma duk inda yayi aiki zakaji kowa na yaba masa kuma nason zama dashi,

Sau tari zakaji yan wasa na maganganun masu horarwa tare da sukan yadda da dama ke gudamar da aikin su amma zaiyi wuya kaji am anbaci Salisu Jegus

Tsohon Mai horarwa Salisu Musa Jegus nada basirar zakulo yan wasa da bunkasa cigabansu kamar yadda duniya tayi sheda, masanin wasan kwallon kafane daya fara yin amfani da matasan yan wasa a jihar kano a lokacin da masu horarwa da dama ke kalubalantar tsarin nasa hakanan shine mai horarwar daya fara kirkiro kungiyar matasan yan wasa yan kasa da shekaru 15 a cikin wata kungiyar kwallon kafa mai zaman kanta,

Kungiyar Dabo U-15 kungiyace daya kirkiro a shekara ta 2011 da nufin samar da matasan yan wasa da zasuyi gogayya da takwarorinsu a najeriya shirin nasa ya zama abin kwaikwayo da alfahari ga masu kungiyar da yan wasa da kungiyoyi a jihar kano,

A ranar litinin din nan ne kungiyar Gaida United ta gabatar dashi a matsayin Daraktan wasan kungiyar bayan cimma yarjejeniya da hukumomin kungiyar karkashin jagorancin Kabiru Haruna Mahuta

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *