Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon Shugaban Jami’ar Maiduguri dake Jahar Borno Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana yadda Makarantar ta hana Yan ta’addan Boko Haram Shigowa cikin ta.

Njodi Wanda shine Sakataren Gwamnatin Jahar Gombe, ya bayyana haka a wata Lakca da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Kashere ta Shirya dake Jahar Gombe.

Lakcar Mai taken “Jami’o’i a lokacin Yan ta’adda: yanayin da Jami’ar Maiduguri ta fuskanta a lokacin Boko Haram.

Tsohon Shugaban Jami’ar Maiduguri yace, daya daga cikin matakan da Jami’ar ta ajiye domin magance wa Jami’ar shigowar Yan ta’addan Boko Haram shine tafiya da kowa da kowa.

Farfesa Njodi ya kara dacewa, sun kuma shigo da Jami’an tsaro da suka hada da Yansanda, DSS, Sojoji da sauran su, domin karawa masu kula da makarantar karfi domin samun tsaro a Jami’ar.

Ya bayyana cewa, Jami’ar ta kuma sanya jindadin Dalibai a matsayin abinda ta sanya a gaba, ta hanyar ziyartar su lokaci-lokaci zuwa Dakunan Kwanan su, wannan ya taimaka kwara dagaske.

Ya kuma bada tabbacin kudirin sa na inganta harkokin karatu da Cigaban Makarantar ta Kashere, da Malaman ta da Dalibai da inganta jindadin su.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *