Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnan jihar Kaduna, ya karbi bakuncin shuwagabanin tsaro da suka hada da shugaban soji, da shugaban kashe gobara da agajin gaggawa da kuma Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna

A yau Laraba shugaban hafsan soji, Laftanar Janar Farouk Yahaya da wasu manyan sojoji suka ziyarci Gidan Gwamnatin jihar Kaduna inda mukaddashin Gwamna Dr. Hadiza Balarabe ta karbe su.

Hakanan babbar tawagar hukumar kashe gobara da agajin gaggawa a karkashin jagorancin A.C.G Muazu Aliyu Tambari, Kwamandan shiyya na Zone B ya ziyarci Gidan Gwamnatin jihar Kaduna

A makon da ya gabata shi ma Sabon Kwamishinan yan sanda da kuma Kwamishinan yan sanda mai barin gado AIG UM Muri sun ziyarci fadar Gwamnatin jihar.

Kwamishinan wanda ya samu sabon mukamin AIG kuma aka tura shi Zone 13, ya gabatar da sabon Kwamishinan yan sanda, CP Mudashiru Abdullahi.

Duka dai mukaddashiyar Gwamnan jihar Kaduna Dr Hadiza Balarabe ce ta karbe su inda suka tattauna muhimman batutuwa kan tsaro da kuma hanyoyin inganta sha’anin tsaro a jihar Kaduna

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *