Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Lauyoyi 31 daga Arewacin Najeriya sun yanke shawarar tsayawa Abba Kyari domin ganin sun kare mutuncin sa da matsayin sa.

Lauyoyin sun yi hakan ne a matsayin amsa kiran gamayyar kungiyoyin arewa na karewa Abba Kyari hakkokinsa.

Barista Bappah Salisu a madadin lauyoyin ya bayyana cewa kyauta zasu kare Abba Kyari.

Wani rahoton Vanguard ya tabbatar cewa akalla lauyoyin Arewacin Najeriya 31 sun alanta niyyar tsayawa mataimakin kwamishanan yan sanda Abba Kyari a kotu. Lauyoyin sun yanke shawaran kare jami’in dan sandan ne bisa ga kiran gamayyar kungiyoyin Arewa inda ta bukaci a kare hakkokin Kyari.

Barista Bappah Salisu wanda ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a yau Labara 11 ga Agusta, inda ya ce zasu kare Abba Kyari kyauta.

Salisu wanda yayi magana a madadin lauyoyin yace an zabe su daga jihohin Arewa daban-daban, kuma akwai kura-kurai a bukatar da FBI tayi na a turo mata Abba Kyari.

Abba Kyari wanda ya sha yabo ciki da wajen Najeriya wajen yaki da ta’addanci a Najeriya an dakatar da shi ne akan ya amshi cin hanci da rashawa a hannun dan damfara Huspuppi ne.

©Zinariya

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *