Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Yayin da taka ledar siyasa ke cigaba da murzuwa a fagen siyasar Jihar kano mataimaki ga gwamnan kano kan yada labarai Aminu Black Gwale yace hakkin sune kare mahibba da martabar gwamnatin kano daga kowane irin hari da yan adawa ke kawowa gwamnatin,

A wata hira ta musamnan da express radio a ranar litinin 9/8/2021 Aminu Black yayi martani ga abokan burmi tare da jan hankali ga yan siyasa da suke cikin gwamnatin dasu fito dan maida martani ga yan adawa da suke sukan gwamnatin a wannan lokaci,

Aminu Black wanda yayi fice wajen tallata aikin gwamnatin APC da Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje yace ” babu wanda ya isa ya hanashi tallata ayyukan alheri da Ganduje yayi, kuma ayyukan ai a fili suke kowa yana gani saida hasada ” inji Aminu Black

Kan yadda ake gudanar da siyasa a jamiyyar Aminu Black cewa yayi shugabannin jamiyyar na gudanar da shugabanci yadda ya dace kuma jamiyyar na tafiya a kwadabe mai tsari da tsafta illa yan gaza gani dake da wata manufa wacce Black din yace bazasu cimma buriba ” mu jamiyyarmu ta masu akidar Ganduje ce kuma Ganduje shine Gwamna kuma muna biyayya ga gwamnati ko yau ko gobe duk wanda zai taba mahibbar gwamnati to zamu saka kafar wando daya kowa nene” inji Aminu Black

Dayake amsa tambaya kan yadda suke sainsa da wani tsagi kan batun fidda dan takarar gwamna a kano Black cewa yayi ” Babu wanda zai iya kwatar wancan dan takara a hannusu kuma batun fito na fito a fagen siyasa ga fili ga mai doki”

Aminu Black wanda a ja kunnen masu adawa da gwamnatin yace lokaci yayi da zasu daina tunda aiki shike nuna irin nagartar gwamnati to shugabancin gwamna Ganduje ya ciri tuta inda yace aikin sa ya dame na kowa a tarihin jihar kano,

Daga karshe Black ya godewa alummar jihar kano bisa goyon baya da suke bawa gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje da adduoi da suke masa abin da yace suna kara karfafawa gwambatin gwiywa,siyasar mu addininmu

Gwamnan mu shygabane  mai hakuri, mutunci da girmama alumma

Gwamna mai aiki da ido zai gani hannu ya taba, ma sanin makamar aiki da kwarewa

Baizo dan ya gina gida ko mota ba, Ganduje jejine baa yimasa kyaure  inji Black Gwale

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *