Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wata kungiya mai rajin bunkasa cigaban kwallon kwando da zakulo matasa masu basira a wasan mai suna African Children Talent Development Foundation (actdf )da Noah Dallaji da hadin gwiywar tsohon kyaftin na kungiyar kwallon kwando ta Kasa Olumide tace ta sunzo jihar kano ne dan shirya wata gasar kwallon kwando ga wasu fitattun jihohin Atewa da zakulo yan wasa dake da basirar wasan amma basu da gata,

A tattaunawarsa da manema labarai yayi gabatar da shirin a garesu Abubakar Muhammad Anbursa yace ya zama dole a garesu su shiga cikin harkokin tallafawa yara da suke da basira amma basu da karfin da zasu iya matsawa gaba a wasan ko kuma samun wata dama ta karatu duk da irin dinbin basirar da suke da ita,

i

Kan yadda gidauniyar Injiniya Noah Dallaji ta bugi kirjin daukar nauyin gasar …..cewa yayi shi Noah a killum burinsa shine yaga ya tallafawa marasa karfi domin su dogara da kansu kuma dayake mai shaawar wasane ya dubi irin tasirin da wasan ke dashi na bunkasa rayuwar alumma musamman idan aka dubi irin su Olumide wadanda wasan yayi musu riga da wando inda suka zama abin alfahari, kwaykwayo da misali a ko ina a fadin duniya,

Anbursa Ya kara da cewa Noah Dallajji mutumne da koda yaushe yake son yaga ya tallafi rayuwar mabukata musamman matasa, shi yasa aka shirya wannan gasa da zaa shafe kwanaki bakwai dan samun zakara, tare da sanya ido dan zakulo matasan da zasuyi fice da samun makoma mai kyau nan gaba,

Dagane da zabin jihar kano a matsayin inda zaayi gasar Abubakar Anbursa cewa yayi ya zame mana wajibi muzo kano dan idan ana maganar kwallon kwando dole sai an sa Kano zancen zai cika, saboda yadda wasan kwallon kwando yake da tasiri a tarihin jihar,

Inda ya kara da cewa manufofin sanya gasar a bayyane suke, ” Tallafawa matasa dake da basira marasa gata i dan ci burinsu”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *