Gwamnan Jahar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci taron masu ruwa da tsaki na Lafiya a Matakin na Shekarar 2021, Wanda ya gudana a Dakin taron na Coronation dake gidan Gwamnatin Jahar Kano.
Taron nada manufar inganta Lafiya a Matakin Farko, wajen cimma Harkokin lafiya a mataki na bai daya na duniya, ta hanyar shirin tabbatar da aiki yanda yake wato-Minimum service package MSPS.
A lokacin taron, Gwamnan ya bayar da takardun daukar aiki ga Kwararrun Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya guda 56, wadanda zasu yi aiki da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jahar.
Bayar da takardun daukar aikin, wani bangare ne na kudirin Gwamnatin Ganduje, wajen bunkasa harkokin Lafiya a Jahar.
A jawabin shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada cewa, taron babu kokwanto zai habbaka cigaban Harkokin Lafiya a Matakin Farko musamman ga Al’ummar Jahar Kano, tare da tabbatar da cimma nasarori a bangaren lafiya.
Daga cikin wadanda suka yi jawabi a lokacin taron sun hada da; Kwamishinan Lafiya da Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko, da Wakilin Ministan Lafiya, da sauran su.