Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban hukumar kula da titina da ababan hawa ta jihar kano kuma shugaban kungiyar kwallon kafar hukumar Karota Dr Baffa Babba Dan’agundi yace hukumar karota ta shirya tsaf dan tunkarar kalubalen dake gabanta a wasan farko da zaa fafata tsakanin hukumomin tsaron dake  jihar kano, da hukumar wasanni ta jihar kano ta shirya,

Da yake tattaunawa da wakilin Express Radio Salisu Musa Jegus, shugaban hukumar karota Dr Baffa Babba cewa yayi tuni hukumar karota tayi nisa wajen sanin mahimmancin wasanni tsakanin maaikatanta. wanda hakanne yasa hukumar ta sauya fasalin kungiyar wasan kwallon kafar hukumar dan tafiya dai dai da zamani,

Da yake karin haske kan yadda aka sauya fasalin kungiyar,  Baffa Babba cewa yayi  “tun bayan shigowata ofis, ni mai son harkokin wasanni ne da taimakawa matasa yan wasa duk da cewa banyi Ball ba, amma ina sonta. to hakanne ya sanyani kafa sabon shugabanci na masana  wasan kwallon kafa inda muka chanja fasalin kungiyar tare da sanya musu alawus duk wata dan  karfafa musu gwiywa yadda zasu iya gogayya da kowace kungiya koda ko kano pillars ce” inji Baffa.

Kan yadda wannan tsari ya sauya tunanin yan wasan, Baffa Babba cewa yayi daga lokacin da muka fara bawa wadannan yan wasa alawus komai ya sauya, kuma abin da yasa na bijiro da basu wannan alawus shine dan na rage musu radadin rayuwa tare da tallafa musu kan abin da suke so suci arzikinsa wato wasan kwallon kafa kuma nagode Allah hakan ya tabbata da goyon bayan sauran maaikatana,

Kan yadda hukumarsa zata tunkari wasa tsakanin manyan hukumomin tsaro dake jihar kano Dr Baffa cewa yayi ” kai kasan bama jin tsoro ko shakka,  wajen gudanar da aiki, kuma duk abin da mukasa a gaba sai mun sami nasara, to hakama wannan wasannin ina tabbatar maka cewa karota zata taka rawar gani kuma zamu lashe gasar a kowane mataki saboda yadda muka horar da yan wasan da zasu wakilce mu,

Kuma mu dama can a tafiye muke kullum kuma ina tabbatar maka da sauran alumma cewa yan wasan hukumar karota sun san girman wakilcin da zasuyi saboda haka bana shakka yan wasana zasu fidda mara da kunya,

Hukumar karota da sojojin sama ne zasu fafata a wasan bude gasar wasannin a ranar 31 ga watan Yulin da muke ciki na 2021 a filin wasa na sani abacha dake jihar kano

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *