Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A yayin da gwamnatoci a matakin kasa da jihohi ke kokawa na rashin shigar kamfanoni da masu hannu da shuni cikin harkokin wasanni kamar yadda yake a kasashen Turai, Amurka da Asia da wasu kashen Afrika ma, sai ga kamfanin Royal Foam ya tsunduma cikin tallafawa harkar,

A wata tattaunawa da wakilin Express Radio Salisu Musa Jegus yayi da Captain Ibrahim Adami na sashin Tennis na Kano Club a yayin da ake gudanar da gasar da ya dauki nauyinta inda ya bayyana kamfanin Royal Foam a matsayin daya daga cikin wandanda suka bada gudummawa dan gasar ta kankama , Captain Ibrahim yace ba wannan ne karon farko da Royal Foam din ke bada gudummawa a harkokin wasa ba, inda ya kara da cewa kamfanin dake samar da Katifa da filalluka dan jin dadin alummar Najeriya da wasu makotan kasashe ya dade yana bada gudummawa ta karkashin kasa wajen bunkasa cigaban wasanni,

Wani binkice da Express Radio ta gudanar ta gano cewa a shekaru kimanin 5 da suka gabata an hango wata kungiyar kwallon kafa dake buga wasa a matakin kasa a ajin matasa dauke da sunan wannan kamfani ” “Royal Foam fc ” inda aka tabbatarwa da majiyar tamu cewa kamfanin ne ke daukar nauyin kungiyar har zuwa wannan lokaci, abinda ya tabbatar da waccan magana da Captain din keyi na yadda kamfanin ke taimakawa harkokin wasanni,

Tunba yanzu ba gwamnati da hukumomin wasanni a jihar kano ke ta kiraye kiraye ga kamfanoni dan su shiga cikin harkokin wasanni amma shiru kake ji, in banda irin su kamfanin Royal foam din da tuni sukayi gaba wajen karbar wannan kira,

Captain Ibrahim wanda ya yabawa kamfanin bisa irin gudunmawar da suka bawa wannan gasa yace gudunmawar tasu wata abar alfaharice da masu shirya wannan gasa ta Kano Club Tennis Championship bazasu manta da ita ba,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *