Bayan shafe kimanin watanni 3 ana fafatawa tsakanin fitattun kungiyoyi sama da 20 dake yankin karamar hukumar Dawakin kudu dan cin kofin shugaban karamar hukumar karo na farko, kungiyar Jido Warriors ksrkashin Jagorancin Auwalu A.A Jido wakilin dagacin Jido ce tayi nasara a wasan karshe da suka fafata tsakanin su da makotan su Yagaya United daga garin Yar Gaya daci 2-0,
A jawabin sa yayin rufe gasar shugaban karamar hukumar Nasiru Ibrahim.Matage ya bayyana wasan da cewa wata yar manuniya ce dake haska irin baiwar da Allah yayiwa karamar hukumar ta hazikan matasa da suke da basira a fagen wasan kwallon kafa abin da shugaban yace bazaiyi kasa a gwiywaba wajen. talkafawa bukatun matasan ba dan kara zaburar dasu, daga nan sai ya taya kungiyar Jido Warriors Murna lashe kofin inda ya bayyana kungiyar da cewa ta zama tauraruwa mai haska karamar hukumar a fagen wasan kwallon kafa bama a dawakin kudu ba har a jihar kano baki daya duba da irin yadda kungiyar ke taka rawa tsakanin. manyar kungiyoyi a jiha,
Shikuwa shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta jihar kano Sharu Rabiu Ahlan wanda ke zaman babban bako a wasan karshen yabawa kungiyoyin yayi bisa irin yadda suka taka leda inda yace kungiyoyin sun cha chanci kaiwa wasan karshen sannan ya yabawa shugaban karamar hukumar Nasiru Ibrahim Matage da shugaban hukumar wasan kwallon kafa na karamar hukumar Maisikari Tsakuwa tare da kira ga shugabancin majalisar karamar hukumar dasu tallafawa kungiyoyin dan rage musu radadi a lokacin da zasu wakilci karamar hukumar a manyan gasa da suka sami chan chantar shiga da hukumar wasan kwallon kafa ke bawa kungiyyo saboda bajintarsu a irin wadannan gasa,
Shikuwa jagoran gasar kuma shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta Dawakin kudu Maisikari tsakuwa godewa shugabancin karamar hukumar dana. Hukumar kwallon kafa ta jihar kano yayi bisa irin goyon baya da karfin gwiywa da suka bayar har wasan ya kamnala, inda yace hakan abin a yaba ne.
Manyan baki da damane daga ciki da wajen jihar kano suka halarci wasan karshen da suka hadar da shugaban shugabannin hukumomin wasan kwallon kafa na kasa Ibrahim Gusau da sakatare hukumar wasan kwallon kafa ta jihar kano Shehu Buhari da Zaharadden Sale Shygaban kungiyar Marubuta Labarin wasanni na kasa reshen jihar kano da wakilcin shugaban karamar hukumar birnin kano Habulele da na karamar hukumar shanono da shygabancin kungiyar magoya bayan kano pilkars Karkashin jagorancin Bashir Idris Maazu Jide da sauran masu ruwa da tsaki a wasan kwallon kafa a jihar kano da karamar hukumar Dawakin Kudu