Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wata kungiya mai suna National First Movement, ta nuna goyon bayanta ga gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya ce mulkin karba-karba ya saba wa kundin tsarin mulki.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa cancanta da karfin isar da aiki su ya kamata su mamaye sararin siyasarmu yayin da 2023 ke gabatowa, jaridar Daily Trust ta ruwaito

.Kungiyar ta nuna goyon bayanta ga takarar Gwamna Yahaya Bello a matsayin shugaban kasa a 2023 Hoto: Alhaji Yahaya Bello

Ta gargadi masu ruwa da tsaki a kasar da su fifita cancanta da kwarewa yayin da zabukan 2023 ke gabatowa don magance dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta.

Ta nuna rashin amincewa da kiran da Ohaneze Ndigbo ta yi kwanan nan cewa a mika mukamin Shugaban kasa zuwa yakin Kudu maso Gabas, tana mai bayyana kiran a matsayin abin da ya saba wa kundin tsarin mulki.

A wata sanarwa a ranar Laraba ta jagoranta, Chris Nwaokobia Jnr, kungiyar ta yi ikirarin cewa taron 1998 a Hukumar Jami’o’i ta Kasa, Abuja wanda Ohanaeze Nd’Igbo ya ambata bai sasanta batun shugabancin karba-karba ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *