National Flag (Tutar Kasa) wata alama ne na girma, martaba da mutuncin kasar, wulakanta ta wulakanta kasar ne da kuma rashin kishi, girmamata kuma girmama kasar ne da kishin ta.
Tutar Nigeria na daya daga cikin tutocin da yanzu haka suke a kafe a Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Washington.
Kashi na 2 (Chapter ii) Karkashin Sashi Na 23 zuwa 24 na Kundin tsarin Mulkin Nigeria (Wato Constitution) ya bayyana cewa dole ne ga kowanne dan Nigeria ya girmama tutar kasar, hade da National Anthem, National Pledge da Sauran su.
Shiyasa ma zakuga idan ana rera taken kasar (National Anthem) ake nutsuwa tare da tattara hankali wuri daya har sai an gama.
Sai dai wasu marasa kishin kasar sukan wulakanta wasu National Ethics na kasar, Kamar: tutar Kasar, National Pledge, National Anthem da sauran su, wanda yin hakan ya saba ma dokokin Nigeria ta kowace fuska.
Domin kuwa kasashe da dama basa lamuntar Wannan aika-aikar. Idan muka dauki Kasar Nijar Misali, ko aibata kasar su kayi to hakan zai iya jaza maka dauri, idan kuma karatu ne ya kaika kasar, to Shikenan ka kawo Karshen zamanka dasu kenan, dole ka bar masu kasar su.
Bisa wannan, gwamnatin Nigeria ta Samar da wata doka mai suna “FLAGS AND COATS OF ARMS ACT” domin kare martaba da mutunci da kimar kasar.
Wannan Kundin dokar yazo da haramcin wulakanta tutar kasar ko wasu National Ethics.
Idan ka duba Sashi Na 7 na wannan kudin (FLAGS AND COATS OF ARMS ACT) ya bayyana cewa haramun ne mutum ya wulakanta tutar Kasar ta kowanne fuska.
Inda shikuma Sashi Na 10 na dokar ya bayyana irin hukuncin dake kan wanda ya wulakanta tutar Kasar da cewa zai biya tarar Kudi Naira Dari Kacal.
Saidai a Shekarar 2016 wani Dan Majalisa mai Suna Hon. Nnenna Elendu Ukeje yakai korafi gaban Majalisa ganin yadda wasu ‘yan kasar suke wulakanta National Ethics na Kasar, inda ya bukaci da akara yawan tarar kudin daga Naira Dari zuwa dubu Dari biyar ga duk wanda ya wulakanta tutar Kasar, ko kuma zama gidan Maza na tsawon Shekara 5, ko kuma a hada ma mutum duka (Tarar Naira Dubu Dari 5, da zama gidan Maza na tsawon Shekara 5), kuma dokar ta samu tsallakewa.
Wulakantawar ya danganci mutum ya yaga tutar, ko ya Kona ta, ko ya cillata a Juji da niyyar wulakantawa, ko ya zana ta ba yadda take ba, ko ya canja mata Color kamar yadda yazo a cikin Bill din da Dan Majalisar ya gabatar Kashi na 8 karamin Sashi na 1 “a” a cikin Baka, zuwa “c” (Section 8 Subsection (1) a to c).
Saidai Karamin Sashi na 2, Karkashin Sashi na 8 “d” “e” ya bayyana cewa banda inda ya kasance tutar ne ta tsufa misali, ko ta lallace, ko kuma takardar da tutar take a jiki ta lallace, ko kuma ginin da aka zana tutar ne ya fadi, to wannan duka babu laifi.
Sannan Sashi Na 8 Na Flags and Coat of Arms Act ya bawa kowanne Jami’in Dan Sanda (Karami ne Ko Babba) damar Karbe duk wani Abu da aka lika masa tutar Nigeria amma da niyyar wulakantawa.
Shehu Rahinat Na’Allah
16th July, 2021.