Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kyaptin na sashin tennis dake kano club a jihar kano Ibrahim Adamu yace babban burinsa shine yaga an bunkasa wasan tennis tsakanin alumma daban daban a jihar kano sabanin yadda wasan ke zama a kebe,

Da yake bayani yayin taron manema labarai kan wani wasa daya shirya a filin wasa na kano club Ibrahim Bayyana makasudin shirya gasar ta ” KANO TENNIS CHAMPIONSHIP ” yayi da cewa wata damace da zata jawo hankalin mutane da dama da zasu shiga cikin wasan tennis sabanin yadda wasu ke nisanta da wasan,

Da yake karin haske kan yadda wasu ke kallon filin kano club Ibrahim Adamu cewa yayi da mutane zasu shigo cikin filin dan ganewa idonsu abin mamaki na yadda wasanni suke a cikin filin sabanin hagen da suke masa inda ya lissafa wasanni irinsu Tennis,Squash, scramble, Table Tennis da cewa duk akwai gamai bukatar yi amma rashin sani ya sanya mutane basa zuwa inda yace wannan wata damace da mutane gari musamman jamioi , hukumomin tsaro da ireirensu zasu dinga zuwa,

Da yake amsa tambaya kan yadda wasan zai kasance captain Ibrahim Adamu cewa yayi da yake wannan shine karon farko an gayyaci manyan mutane da dattijai dan shiga gasar daga jamiar Bayero, Airforce base da labanon club dan gwaji, kuma haka zai bada dama ga kowa dan zama member,

Kan yadda gasar take Captain Ibrahim cewa yayi shekaru 25 da suka gabata kamfanoni kan dauki nauyin gasar a wancan lokaci amma yanzu haka yaci tura saboda matsin tattalin arziki abin daya sanyashi yunkurin dawo da gasar da yake sa ran gudanar da ita duk shekara a matakai daban daban,

Kyaututuka da dama za aci a yayin gudanar da gasar da za’a fara 24 ga watan Yuli zuwa 31 ga wata wato kwanaki 7 dai dai.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *