Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Yayin da sallar layya ta bana ta rage kwanaki kadan sai gashi dabbobi sunyi tashin gwaron zabi da masu sanaar sai da dabbobi musamman raguna ke cewa basu taba ganin yadda raguna da sauran dabbobi sukayi tsada ba kamar wannan shekara ta 2021,

Wani da muka zanta dashi a kasuwar saida dabbobi dake kofar naisa Malam Sani Musa yace yakai shekara 30 yana saida dabbobi a bakin kofar naisa tun ana daure raguna a lokacin sallah kawai amma bai taba ganin yadda dabba ke tsada ba kamar wannan shekara, inda yace da ana tsammanin idan akayiwa maikata albashi kasuwar zata samu amma sai gashi anyi albashin amma maaikata sun shamuke sunki siyen ragunan kuma idan kace meya hanasu siyen rago sai suce tsadarsa kuma gara su sayi abinci dasu sayi rago duk da shima abincin na tsada,

Malam Sani ya kara da cewa a waje Daya suma masu ragunan sunci buri kuma ma ai ragunan baa tasu zakaga shanu da rakuma ne akafi kawowa to ko suma da mutane ke hada kudi suyi watanda to bana dai sai a hankali inji Malam Sani.

Da muka tambayeshi to ko yaya yake ganin yadda kasuwar zata kaya zuwa jajibere Mal Sani cewa yayi babu tabbas na yadda kasuwar zata kasance dan mutane babu kudi a hannunsu,

Rago a bana na 50,000 ma ai shine koma baya amma harda na 200,000

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *