Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati da Tattalin Arziki (EFCC) ta mayar da martani ga rahoton jaridar Peoples Gazette game da cewa hukumar na shiga cikin sirrin wadanda ake zargi, a wasu lokuta tana shiga fasa dakin hotel hotel ba tare dana Cikin dakin sun shirya ba.

Mai magana da yawun hukumar yaki da cin hanci da rashawa Wilson Uwajaren, ya fada wa jaridar Punch cewa hukumar ta lura cewa wasu daga cikin masu Laifi suna amfani da mata tsirara a matsayin garkuwa a yayin da hukamar ta kai hare-haren samame, saboda haka jami’ai ke yawan shiga ba tare da bata lokaci ba don hana su lalatar

A ranar Talata, shaidu sun gaya wa jaridar Gazette cewa, baƙi da yawa a otal ɗin sun shiga damuwa bayan da jami’an hana cin hanci da rashawa suka keta sirrinsu da sanyin safiyar a Otal ɗin Parktonian da ke Legas

Sun fadawa jaridar The Gazette cewa wasu daga bakin sun yi tsirara lokacin da wakilan da suka yi ikirarin suna farautar wadanda ake zargi da damfara ta yanar gizo suka kutsa kai suka hana su sutura kafin a musu tambayoyi.

“Sun kutsa cikin otal din kuma sun yi barazanar harbe masu karbar baki da gudanarwa idan ba su hanzarta sakin musu katin shiga ba,” in ji wani ganau. “Don haka dole ne ma’aikatan otal din su yi biyayya nan da nan.”

“Sun ci gaba da binciken wasu dakunan. Sun tafi tare da kimanin mutane 13, ”in ji wani ganau.

Sai dai, da yake kare matakin da aka bayyana a matsayin “haramtacce”, Mista Uwujaren ya bayyana cewa wadanda ake zargi da aikata laifuka ta hanyar amfani da yanar gizo na tura mata zuwa ga tsiraici don bata hankalin masu gudanar da aikin, ta yadda za su lalata hujjoji.

“Amma hukumar ta lura da wani abin da ya zama abin damuwa wanda a yanzu haka wadanda ake zargi da aikata laifuka ta hanyar amfani da yanar gizo ke amfani da matan da ke cikin tsiraici a matsayin yaudara don bata hankalin jami’an hukumar don ba su damar rusa shaidun da ke gabanta kamun,” in ji Mista Uwujaren.

Ya yi ikirarin cewa jami’an sun yi aiki ne a kan bayanan sirri da aka kai wa wadanda ake zargi da damfara ta intanet a otal din, kamar yadda ya lura cewa an kama 30 da ake zargi.

Mista Uwujaren ya kara jaddada cewa “an aiwatar da aikin ba tare da wani tashin hankali ba kasancewar an sanya ido a wurin tun makonnin baya inda hukumar ta samu damar kebe dakunan da aka kama wadanda ake zargin.

“Samun damar shiga cikin dakunan ba shi da wata illa kasancewar hukumar tana da hanyar da ta dace don isa irin wadannan wuraren ba tare da amfani da karfi ko rashin jin dadi ga bakin ba. Babu baƙon otal ɗin da aka tozarta.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *