La’akari da halin da aka shiga na zafin aski idan yazo gaban goshi kamar yadda masu magana ke fadi akwai bukatar gwamnatin jihar kano karkashin jarumin gwamna kuma masoyin harkkokin wasa da bunkasa cigaban matasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya waiwayi kungiyar kwallon kafa ta kano pillars kan irin halin da take Neman fadawa a lokacin da aski yazo gaban goshi a gasa 2 da kungiyar ke taka rawar gani Gasar NPFL da Gasar cin Kofin Ateo,
Wani bincike da sashin wasanni na express radio ya gudanar ya gano cewa yan wasan kungiyar na taka rawar gani wajen fidda mara Da kunya wajen samun nasara a wasanninsu gida da waje haka kuma shugabancin kungiyar karkashin jagorancin Surajo Shuaibu Yahaya Jambul nayin kokari wajen karawa yan wasan karfin gwiywa amma hausawa na cewa da ruwan ciki ake jan na rijiya,
Rahotanin sun cigaba da cewa kawo iyanzu yan wasan kungiyar na bin bashin kudin garabasar wasa na wasanni .18 ba tare da anbiyasuba wasuma na cewa kusan wasanni 21 duk da irin yadda mukasan yadda gwamnan Abdullahi Umar Ganduje da son kungiyar Kano Pillars sai gashi kungiyar na rasa irin abubuwan da shi gwamnan da kansa ke yimata a lokacin da yake mataimakin gwamna,
Tarihi ya tabbatar da cewa kungiyar ta kano pillar madubi ce ga kungiyoyin kwallon kafa a fadin kasarnan idan ka cire kungiyar Enyimba da ire irensu kuma kungiyace da take wakiltar arewacin najeriya kasancewar kungiyace da dukkannin kungiyyoyin arewa ke kyaikwayonta a kowane mataki,
Kawo iyanzu da wannan rahoto ke fita akwai zargi mai karfi na cewa kungiyar ka iya samun koma baya a dukkannin wasanninta laakari da halin da kungiyar ke ciki na rashin kudi da kungiyar ke bukata na karin karfi,
Wani wanda muka tattauna dashi kuma ya nemi mu sakaya sunansa yace kungiyar bata taba shiga halin tasku ba irin wannan lokaci duk da irin kokarin da yan wasan keyi da kishin kungiyar da jihar kano ne kawai amma halin da suke na bukatar kulawar gwamnati musamman mai gayya mai aiki gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje,
Mutumin ya kara da cewa sau 2 yana ganin Dr Abdullahi Umar Ganduje na bin kingiyar Pillars dan karbo kofin Firimiya lokacin yana mataimaki inda yace yana da labarin cewa Dr Abdullahi Umar Ganduje yasha bawa kungiyar da yan wasan kungiyar kudade a cikin aljihunsa, abinda yabawa mutumin damar kiran masu ruwa da tsaki dasu kawowa kingiyar daukin gaggawa,