A ranar Litini din da ya gabata ne kotu dake karamar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa ta yanke wa wani dattijo mai shekaru 65, Sabiu Suleiman hukuncin zama gidan kaso har sai bayan rai a dalilin samun shi da aka yhi da laifin yin luwadi.
Alkalin kotun Ubale Musa ya yanke wannan hukunci ne bayan shaidu su tabbatar cewa an kama shi turmi da tabarya yana aikata wannan lalata da wani yaro dan shekara 15.
A zaman shari’a fannin shigar da kara ya gabatar da shaidu hudu sannan fannin dake kare Suleiman auka gabatar da shedu 3.
Bayan haka kakakin ma’aikatar shari’a Zainab Baba-Santali a wani takarda da aka raba wa manema labarai ta ce hukuncin zai zama darasi ga mutanen dake da niyya ko kuma suke aikata irin haka a jihar.
Zainab ta kuma bayyana cewa kotun a ranar 18 ga Yuni ta yanke wa wani Samaila Bello hukuncin daurin rai da rai.
Alkalin kotun Hussein A. Mukhtar ya yanke wannan hukunci ne bayan an kama shi da laifin hada baki aka cuci wani da aikata fashi da makami.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta fitar da rahoton cewa fyade ya zama ruwan dare a jihar.
Rundunar ta sanar cewa a jihar fyade ya yi kamari domin ya fi wasu laifuffuka kamar su garkuwa da mutane da kai wa mutane hari aukuwa.
Bisa ga rahoton rundunar ta saurari kararrakin fyade 35 a cikin watanni hudu a jihar.