Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wani tsohon dan majalisan jihar Kogi, Friday Makama Sani, da abokansa shida sun shaki kamshin yanci bayan garkuwa da su da wasu yan bindiga sukayi a Abuja.

Friday Makama tare da abokan nasa sun kubuta ne bayan biyan yan bindigan kudin fansa. Jaridar Tribune ta ruwaito cewa sai da aka biya yan bindigan kudi milyan 15 da katin waya na N100,000.

Yan bindigan da farko sun bukaci a basu N20 million. Majiyoyi daga iyalan wadanda aka sace sun tabbatar da cewa an sakesu ranar Asabar.

Wasu yan bindiga sun kai farmaki gidan Otal na Hilltop dake garin Tunga Maje a birnin tarayya Abuja da daren Laraba, 24 ga Yuni, 2021.

Daily Trust ta rahoto cewa sun yi awon gaba da mamallakin Otal din, tsohon dan majalisa tare da wasu mutane.

An ce mamallakin Otal din mai sune Prince Adejo, tare da wasu mutane shida na ganawa a ciki lokacin da yan bindigan suka kai farmaki. Garin Tunan-Maje ta kwan biyu tana fuskantar barazanar yan bindiga.

A cewar mazauna garin, wannan shine karo na biyar da aka kai hari don garkuwa da mutane a shekarar nan.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *