Abin da ya sa matan da suka yi ilimi mai zurfi, ko na zamani ko na addini, suke bawa wasu mazan tsoro shi ne, su ba za a iya juyasu da yan dabaru kamar yadda za ka iya juya kowace jahila da sunan wayewa ko addini ba.
Matan da suka yi ilimi mai zurfi sun riga sun san yancinsu kuma sun san hakkinsu, sannan sun san me suke yiwa maza da alfarmar soyayya ce ba wai dole ba ne. Don haka a lokaci daya za su iya cewa sun fasa kuma ta zauna daram.
Macen da ta yi ilimin addini mai zurfi ta san cewa ciyarwarta da tufatarwarta duk a hannun mijinta yake. Ko girkin da take masa alfarma ce kawai ba dole ba. Maimakon a raina mata hankali a ce ta dinga wanke kayan mijinta da sunan wanke zunubi, ta san mijinta shi yake da hakkin dinka mata kayan idan bashi da kudin kai wanki to shi zai wanke mata su. Duka a karkashin tufatarwa yake. Shi ya wanke zunuban nasa.
Wacce ta yi ilimin zamani ta san me ake nufi da shari’a, ba yadda za a yi mijinta haka kawai ya saketa ya kwace mata yaya ya bawa kishiyarta. Kotu za ta kaishi a barsu a hannunta har sai sun kai shekarun da shari’a ta gindaya tukun sannan za a mayarwa da mijin. Kuma dole ya dinga biyan kudin ciyar da su duk wata ko duk sati.
Idan kin yi ilimin addini mai zurfi babu yadda mijinki kawai zai tashi da safe ya ce ya sakeki ki tashi ki bar masa gida kafin ya dawo daga kasuwa. Zama za ki yi daram har sai kin gama idda a gidansa. Ko bai mayar da ke ba ai kin bata masa rai ta hanyar wajabta daga bikin da ya shirya. Idan kuma ya sake ko marinki ya yi to dama kilu ta ja bau tun da yanzu ba aurenki yake ba balle ya ce ya daki banza.
Wadannan yan kadan kenan da na san cewa da mata suna ilimi mai zurfi da ba za a dinga raina musu hankali ba. To amma maza sun fi son jahila saboda tafi dadin sha’ani. Kana cutarta tana cewa ibada take. Kana zalintarta kana cewa wanke zunubanta take. Akan abin da wajibinka ne sai ka saketa ka ce ta kasa yi. Nawa ka sani sun saki matansu akan girki? To wannan shi yasa za ka ji wasu mazan na cewa gwanda jahila da mai ilimi.